Shugaba Bola Tinubu: Najeriya za ta himmatu wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da ta kulla da kasar Burtaniya
2024-11-05 10:44:03 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa, Najeriya za ta himmatu sosai wajen aiki da sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa da ta kulla da kasar Burtaniya a fagen ayyukan da za su amfani rayuwar al’umma.
Ya tabbatar da hakan ne jiya Litinin 4 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin sakataren kula da harkokin kasashen waje na Burtaniya Mr. David Lammy.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatin Najeriya za ta kyautata goyon bayanta ga wannan yarjejeniya domin dai samun ci gaban kasa baki daya.
Shugaban na tarayyar Najeriya ya yi kira ga kasar ta Burtaniya da ta kara karfafa dangantakarta da kasashen Afrika musamman ma dai kasashen da suke fuskantar rikice-rikice kamar Sudan ta hanyar ayyukan jin kai.
Haka kuma shugaba Bola Tinubu ya shaidawa sakataren harkokin kasashen wajen na Burtaniya cewa, kasashen yammacin Afrika suna matukar fuskantar kalubalen tsaro, sannan kuma suna samun karuwar ’yan gudun hijira wadanda aka sari suna zuwa ne daga kasashen Mali da Burkina Faso, a don haka akwai matukar bukatar kasar ta Burtaniya ta yi kokari wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin kasashe na Afrika. (Garba Abdullahi Bagwai)