logo

HAUSA

Wakilin Sin: Mafitar rikicin zirin Korea na hannun Amurka

2024-11-05 13:00:20 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce kashin bayan rikici zirin Korea shi ne rikici tsakanin Amurka da Korea ta Arewa, kuma mafita ga matsalar na hannun Amurka.

Wakilin na Sin ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin taron Kwamitin Sulhu na MDD game da batun nukiliyar Korea ta Arewa, inda ya yi kira ga Amurka ta yi watsi da munanan ayyukanta kamar na matsin lamba da barazana da kirkiro yanayin warware matsalar cikin lumana ta hanyar tattaunawa.

A cewar Fu Cong, Sin ta yi ammana cewa Kwamitin Sulhu na da muhimmiyar rawar takawa game da batun na zirin Korea.

Ya kuma nanata cewa, a matsayinta na makwabciya ta kurkusa, kuma babbar kasa da ta san ya kamata a zirin Korea, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a arewa maso gabashin Asiya. (Fa’iza Mustapha)