Huang Huilin: Kamar 'Kogi mai Fadi da Girma'
2024-11-05 19:46:49 CMG Hausa
Huang Huilin, mai shekaru 90, mamba ce ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wacce ta yi rayuwarta da kyau. A cikin shekarun 1950, Huang ta shiga cikin 'yan sa kai na jama'ar kasar Sin da suka shiga jamhuriyar dimokaradiyyar Koriya (DPRK) don taimakawa al’ummmar Koriya wajen yaki da maharan Amurka. Bayan ta dawo daga yakin kuma ta samu lambobin yabo na soja, ta yanke shawarar sadaukar da rayuwarta ga aikin koyarwa.
A halin yanzu Huang babbar farfesa ce a jami'ar horas da malaman koyarwa ta Beijing (BNU), kuma shugabar kwalejin mu’amala da kasa da kasa kan al'adun kasar Sin (AICCC).
A cikin shekaru sittin da suka gabata, Huang ta taimaka wajen kafa tsarin nazarin wasan kwaikwayo, fina-finai da shirye-shiryen talabijin. Da yin haka, ta zama malama ta farko dake koyar da dalibai masu neman digirin digirgir a fannin nazarin ilmin fina-finai a kasar Sin.
Madam Huang Huilin ta kuma kafa kungiyar wasan kwaikwayo ta daliban BNU a 1980s; A shekarar 1993, ta taimaka wajen kaddamar da bikin fina-finai na dalibai na jami'o’in Beijing. Tun daga wannan lokacin, ta taimaka wajen aiwatar da jerin shirye-shiryen cudanyar al'adu, ta yadda ‘yan kasashen waje suka kara fahimtar kasar Sin.
Yayin da take ci gaba da rayuwarta kamar "kogi mai fadi da girma," Huang tana ta bayar da gudummawarta a fannonin daban daban. Yawan shekaru ba matsala ba ce ga Huang. A watan Maris 2024, ta samu lambar yabo ta Mace Mafi Nagarta Ta Sin, a cikin mata goma da suka samu lamar yabo, shekarunta sun fi yawa.
Madam Huang ta bayyana cewa, “Idan aka waiwaya baya, aikin koyarwa ya kasance wani muhimmin bangare na rayuwata. Idan kuma aka hango gaba, zan ci gaba da tafiya a kan hanyar da ke cike da bincike, kulawa mai kyau, da sadaukarwa."
An haifi Huang Huilin a shekara ta 1934 a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin. Ta girma a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, amma ta shiga makaranta a birnin Suzhou na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar. Ta shafe yawancin kuruciyarta tana tafiya tsakanin Tianjin, Beijing, Shanghai da Suzhou. Ta koma Beijing tare da mahaifinta a 1950, kuma ta shiga makarantar sakandare mai alaka da BNU.
Bayan barkewar yakin maharan Amurka don taimakwa ‘yan Koriya, Huang, matashiyar daliba a lokacin, ta nemi shiga cikin 'yan sa kai na jama'ar kasar Sin da ke shiga jamhuriyar dimokaradiyyar Koriya (DPRK) don yin yaki.
Kafin ta tafi fagen daga, Huang ta canza haruffan Sinanci na sunanta, Huilin, daga "慧麟" zuwa "会林" – furtawa iri daya da na farkon amma sun fi saukin rubutawa. Yayin da ta tuna yadda ta yarda da shawarar malaminta ta canza haruffan ba tare da jinkiri ba, ta ce, "’yan uwana masu gwagwarmaya za su iya tunawa da rubuta sunana cikin sauki. Hakan ya taimaka wajen saukin sadarwa a fagen daga. Wannan yana da mahimmanci!"
Huang na daya daga cikin sojojin da suka yi sa'ar tsira daga yakin. Ba za ta taba mantawa da yadda ita da 'yan uwanta suka rika tura kwallayen bama-bamai zuwa fagen daga a lokacin yakin kogin Ch'ongch'on ba. Sama da sojoji 100 daga rundunarta sun mutu a wannan yakin. Huang ta kara da cewa, "Zuwa yaki ya bar ni da kyakkyawar manufa, na cewa dole ne in yi kokari, a tsawon rayuwata, don taimakawa wajen bunkasa ci gaban kasata."
A shekara ta 1954, bayan ta dawo daga yakin, Huang ta ci gaba da karatunta a makarantar da ke da alaka da BNU. Ta samu lambar yabo, a matsayinta na soja mai kwazo na 'yan sa kai na jama'ar Sinawa, da kuma lambar yabo ta soja ta azurfa daga DPRK.
A shekarar 1955, bayan da ta kammala karatun sakandare, Huang ta samu damar shiga sashen nazarin adabin Sinanci na BNU. A shekara ta 1958, bayan ta kammala karatu daga wannan ajin, an ba ta damar koyar da adabin Sinanci na zamani. Daga wancan lokaci, Huang ta kwashe shekaru 66 tana koyarwa a jami'ar.
Yayin da Huang ta zama cikakkiyar malama, ajujuwanta sun shahara sosai. A cikin shekarun 1980, ita da mijinta, Shao Wu, sun kafa kungiyar wasan kwaikwayo ta daliban BNU, wadda ta kasance tushen gagarumin wasan kwaikwayo.
A shekarar 1992, yayin da BNU ke shirin kafa sashen farko na nazarin fina-finai da talabijin a wata babbar jami'a a kasar Sin, shugaban BNU ya zabi Huang ta zama daraktan kwalejin wasannin fasaha, da taimakawa wajen kafa sashen. Huang tana da shekaru 58 a lokacin, kuma shekaru biyu kacal suka rage ta yi ritaya. Duk da haka, ta karbi aikin.
A karkashin jagorancin Huang, kwararriyar farfesa mai himma, a shekarar 1993 BNU ta kafa sashen koyar wa masu neman digiri na biyu da ke mai da hankali kan fasaha da dabarun daukar shirin fina-finai da talabijin. A shekarar 1994 kuma, an fara koyar da daliban da ke neman digiri na rukunin farko ilmin fina-finai da talabijin. A 1995, BNU ta kafa ajin masu neman digirin digirgir a fannin ilmin fina-finai, wanda ya sa BNU ta zama jami'a ta farko a kasar Sin da ta kafa irin wannan ajin. (Kande Gao)