logo

HAUSA

Asusun dake kula da canjin yanayi ya ware Sefa miliyar 29 domin kasashe 4 na UEMOA

2024-11-05 09:52:44 CMG Hausa

Asusun dake kula da canjin yanayi, Green Climate Fund ya amince da ware kudin Euro miliyan 44.02, kimanin Sefa miliyar 29 zuwa ga bankin ci gaban yammacin Afrika BOAD domin wani shirin yaki da rauni da illolin sauyin yanayi a shiyyar yammacin kasashen Afrika.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Bisa taken kari ga ci gaban cikin gida, wannan shiri ya tattara kudin Euro miliyan 52.82 kwatankwacin Sefa miliyar 35, wanda kuma zai gudana bisa tsawon shekaru 5, kuma zai shafi kasashen Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Mali da kuma Nijar, in ji bankin BOAD a cikin wata sanarwar da aka aikewa manema labaru a wannan mako.

A cewar wannan sanarwa, shirin na da manufar saukakawa kananan hukumomi da kuma bangaren masu zaman kansu, musamman ma na wadannan kasashe hudu kai ga kudaden da suka shafi ayyukan dake alaka da yaki da canjin yanayi, ta hanyar wani tallafi na kwarewa, da wani tallafin kudi da kuma bada dama ga karfafa karfin ayyukansu.

Shi dai asusun dake kula da canjin yanayi, ko Green Climate Fund, GCF, wani muhimmin tsarin kudi ne da aka aiwatar a karkashin jagorancin kungiyar MDD da kuma ya kasance wata damar tattara kudade daga wajen manyan kasashe masu ci gaban masana'antu, domin aza su bisa akibla ta yadda za su zuba kudade kan tsare-tsaren yaki da canjin yanayi da kuma kama hanyar juriya da tafiya tare da sauyin yanayi musamman ma a cikin kasashe masu rauni dalilin sauyin yanayi.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.