Xi Jinping ya taya Ratu Naiqama Lalabalavu murnar lashe zaben shugaban kasar Fiji
2024-11-05 16:31:59 CMG Hausa
Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Ratu Naiqama Lalabalavu murnar lashe zaben shugaban kasar Fiji. A cikin sakon da ya aika masa, Xi ya bayyana fatan hadin gwiwa da Fiji, don gaggauta raya huldar abota bisa manyan tsare-tasre a duk fannoni tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, da ma amfanawa al’ummun kasashen biyu baki daya. (Amina Xu)