An kaddamar da taron kasashen duniya karo na 12 kan raya birane a Masar
2024-11-05 09:57:49 CMG Hausa
An kaddamar da taron kasashen duniya karo na 12 kan raya birane, jiya Litinin a birnin Cairo na Masar, kuma wannan ne karo na farko da taron ya koma nahiyar Afrika bayan sama da shekaru 20.
A jawabinsa na bude taron, shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ce taron na bana na gudana a lokaci mai muhimmanci, inda tashe-tashen hankula da ake fuskanta a duniya, ciki har da yaki mai muni, ke da mummunar illa ga al’ummomin birane da garuruwa.
Da yake tsokaci kan yake-yaken dake faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, musammam yakin zirin Gaza da Lebanon, ya bukaci a gaggauta kawo karshen zubar da jini da lalata kayayyaki tare da bin tafarkin sake ginawa da raya yankin.
Taron wanda Masar da shirin raya birane da samar da matsuguni na MDD suka dauki nauyi, zai gudana har zuwa ranar Juma’a. Taron ya samu halartar jami’an gwamnati da masana da ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma da masu tsara birane da wakilan kungiyoyin al’umma.
Wata tawagar kasar Sin karkashin jagorancin ministan samar da gidaje da raya birane da karkara na kasar Ni Hong, ita ma ta halarci bikin bude taron. (Fa’iza Mustapha)