logo

HAUSA

Isra’ila ta sanar da MDD soke yarjejeniyar hadin gwiwa kan aikin ba da tallafi a yankin gabashin gabar tekun Bahar Rum

2024-11-05 10:35:43 CMG Hausa

 

Ma’aikatar diflomasiyya ta kasar Isra’ila, ta sanar a jiya Litinin cewa, bangaren Isra’ila ya riga ya nemi MDD da ta soke yarjejeniyar da ya kulla da MDD a shekarar 1967, kan ayyukan ofis mai kula da ba da tallafi ga ’yan gudun hijira Falasdinawa da wasu ayyuka a yankin dake gabashin gabar tekun Bahar Rum.

A cikin sanarwar, ma’aikatar ta ce, Isr’aila za ta ci gaba da hadin gwiwarta da hukumomin Majalisar kan sauran ayyuka, don tabbatar da baiwa fararen hula dake zaune a yankin Gaza tallafin jin kai. A sa’i daya kuma tana kokarin kawar da barazana da za ta fuskanta. Kaza lika, sauran kungiyoyin kasa da kasa za su maye gurbin wannan ofis.

Rahotanni na bayyana cewa, a ranar 28 ga watan Oktoban da ya gabata, majalisar dokokin Isra’ila ta zartas da wata doka, ta hana ofishin ya gudanar da aikinsa a kasar Isra’ila, da ma dakatar da hadin gwiwar mahukuntan kasar da ofishin. (Amina Xu)