logo

HAUSA

Mambobi 8 na kungiyar OPEC+ sun tsawaita wa’adin rage man da suke samarwa da wata guda

2024-11-04 11:05:52 CMG Hausa

Mambobi takwas na kungiyar kasashe masu fitar da man fetur ta OPEC +, sun tsawaita wa’adin rage yawan man da suke samarwa da wata guda, har zuwa karshen watan Disamba, saboda karyewar farashin man.

Kungiyar OPEC+ ta kunshi kasashe masu fitar da man fetur wato OPEC da kuma kawayenta. Kasashen takwas da suka yanke shawarar rage fitar da man bisa radin kansu, sun hada da Saudiyya da Rasha da Iraqi da Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait da Kazakhstan da Algeria da kuma Oman.

Wadannan kasashe sun nanata kudurinsu na tabbatar da cika mizanin suka tsara na samar da man da kuma daidaita duk wani gibi na samar da man fiye da kima da za a iya samu, zuwa watan Satumban 2025. (Fa’iza Mustapha)