Jiragen saman yaki samfuran B-52 da Amurka ta kara turawa sun isa yankin Gabas ta Tsakiya
2024-11-03 16:49:19 CMG Hausa
Sakamakon yanayi mai tsanani da ake fuskanta a yankin Gabas ta Tsakiya, kwamitin tsakiya na rundunar sojin kasar Amurka ya sanar a jiya ranar 2 ga wannan wata cewa, jiragen saman yaki samfuran B-52 da Amurka ta kara turawa sun isa yankin Gabas ta Tsakiya.
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Amurka Patrick Ryder ya bayar da sanarwa a ranar 1 ga wannan wata cewa, don tinkarar kalubale daga kasar Iran, kasar Amurka za ta kara jibge karfin soja a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da jiragen saman yaki samfuran B-52, da jirgin ruwan yaki da sauransu. An ce, za a jibge su a makwanni masu zuwa, rukunin jiragen ruwan yaki masu daukar jiragen saman yaki na USS Abraham Lincoln ya shirya janyewa daga yankin.
Tun daga barkewar rikicin Palesdinu da Isra’ila na wannan karo a watan Oktoba na shekarar bara, ake tanadar manyan jiragen ruwan yaki masu daukar jiragen saman yaki na kasar Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. An jibge rukunin jiragen ruwan yaki masu daukar jiragen saman yaki na USS Abraham Lincoln a yankin a watan Agusta na shekarar bana. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar, an ce, za a janye rukunin daga yankin Gabas ta Tsakiya tun daga tsakiyar wannan wata, yana yiwuwa ba za a samu manyan jiragen ruwan yaki masu daukar jiragen saman yaki na kasar Amurka a yankin a lokacin ba. (Zainab Zhang)