Masu ruwa da tsaki sun koka kan rashin ingancin abincin dabbobi a Najeriya
2024-11-03 16:35:17 CMG Hausa
Masu ruwa da tsaki a kan harkar kiwon dabbobi a Najeriya sun koka ainun kan rashin ingancin abincin dabbobi a kasar, duk kuwa da mahimmancin da kiwo ke da shi ga harkokin cigaban tattalin arziki.
Sun bayyana wannan damuwa ce a birnin Abuja ranar Juma’a 1 ga wata yayin babban taro na kasa da kasa da kungiyar tarayyar Afrika ta shirya kan batutuwan da suka shafi kiwo da kasuwancin dabbobi a nahiyar.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mahalarta taron da suka fito daga kasashen Burkina Faso da Chadi da Kamaru da Jamhuriyyar Benin da kuma Najeriya sun ce abin takaici ne mutuka ganin yadda masu sana’ar kiwon dabbobi ke cin karo da wahalhalu daban daban wajen samun ingantattun abincin dabbobi, da rashin ma’ajiyar abincin dabbobi na zamani, kana da rashin samun wata sabuwar hanya mafi sauki wajen sufurin shanu zuwa kasuwanni, lamarin da zai kara inganta koshin lafiyar shanun.
Taron ya tattauna sosai a kan tsarin kasuwancin dabbobi a arewacin Najeriya wanda yake tattare da bin matakai masu tsawo musamman wajen jigila tsakanin kasuwannin dake kudancin kasar inda ake shafe dubban kilomita.
Haka kuma mahalarta taron sun yi kira ga mahukuntan kasashen dake nahiyar da su yi kwaskwarima ga tsarin zirga zirga ta kan iyakoki tare kuma da kyautata tsarin kiwon lafiyar dabbobi da kuma gidajen yanka dabbobin.
A jawabin da ya gabatar yayin bude taron, karamin minista a ma’aikatar aikin gona da bunkasa samar da abinci na Najeriya Sanata Sabi Aliyu ya ce a shirye gwamnatin Najeriya take ta kara bunkasa sha’anin kiwon dabbobi a kasar, saboda yadda bangaren ke taka rawa sosai wajen bunkasa harajin cikin gida.
Ya ce daga cikin matakan da gwamnatin ke dauka wajen kyautata sana’ar kiwo a kasar sun hada da samar da damarmaki ga kananan manoma wajen samun na’urorin zamani da za su taimaka wajen saukaka harkokinsu, ta yadda tattalin arzikin su zai yi saurin habaka.(Garba Abdullahi Bagwai)