logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jajantawa sarkin Sifaniya bisa ibtila’in ambaliya

2024-11-02 19:54:48 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa sarkin Sifaniya Felipe VI, sakon jaje, sakamakon ibtila’in mamakon ruwan sama, da ambaliya da ta shafi wasu sassan kasar. 

Cikin sakon da shugaba Xi ya aike a Asabar din nan, ya ce ya kadu matuka da jin labarin aukuwar wannan bala’i, wanda ya haifar da rasuwar mutane da dama da kuma asarar dukiyoyi.

Ya ce a madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, yana mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasu, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Kaza lika, shugaba Xi ya ce yana da imanin cewa, karkashin jagorancin sarki da gwamnatin Sifaniya, al’ummun dake yankin da ambaliyar ta shafa za su kai ga fita daga tasirin wannan bala’i, tare da sake gaggauta gina gidajen su.    (Saminu Alhassan)