logo

HAUSA

An kaddamar da majalissar lura da matsalolin muhalli a tarayyar Najeriya

2024-11-02 16:54:47 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Nijeriya kashim Shettima ya jagoranci kaddamar da majalissar kasa a kan sha`anin lura da matsalolin zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da fari da kuma kwararowar Hamada.

An kaddamar da `yan majalissar ne jiya Juma`a 1 ga wata a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja da nufin shawo kan kalubalen da matsalolin muhalli da sauyin yanayi a Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A jawabinsa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jaddada muhimmancin daukar matakan bai daya wajen maganin munmunan tasirin annobar muhalli wanda yake cigaba da karuwa yanzu haka a Najeriya.

Daga cikin nauye nauyen dake wuyan majalissar sun hada da baiwa gwamnati shawara a game da matakan da za a rinka bi wajen maganin matsalolin muhalli, tare kuma da fito da matakai masu nisan zango da gajeren zango da kuma tsaka-tsaki wajen kare afkuwar duk wata annoba da ka iya shafar muhalli, har ila yau kuma yana daga cikin aikin majalissar kyautata tsarin wayar da kan jama’a a game da yadda za a rinka jure matsalolin sauyin yanayi.

Mataimakin shugaban kasar ya ce yana da kyakkyawan fatan cewa majalissar tana da kwarewar da za ta iya tunkarar dukkan wani kalubale da ka iya faruwa sakamakon sauyin yanayi.

Sabuwar majalissar tana karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa ne yayin da gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da Oyo da Ebonyi da Bauchi da kuma Jigawa za su kasance mambobi. (Garba Abdullahi Bagwai)