logo

HAUSA

Gundumar da ta shahara da samar da jita a kasar Sin

2024-11-01 16:09:07 CRI

Sanin kowa ne jita kayan kida ne da ya samo asalinsa a kasashen yammacin duniya, amma ko kun san a nan kasar Sin, akwai wata gundumar da take sahun gaba a duniya wajen samar da jita, ko ta fannin kayayyakin da ake amfani da su wajen hada jita, ko kuma ta fannonin fasahohi da ma ingancin jita da ya samar. Har wa yau daga cikin ko wadanne jita guda 7 da aka samar a fadin duniya, daya an samar da shi ne a gundumar. Sunan gundumar kuma shi ne Zheng’an, wanda ke lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

A kasance tare da mu cikin shirin, don jin karin haske. (Lubabatu)