logo

HAUSA

Majalissar tattalin arziki ta Najeriya ta bukaci shugaba Tinubu da ya dakatar da shirin samar da dokar sauye sauyen haraji ta kasa

2024-11-01 09:16:49 CMG Hausa

Majalisssar lura da harkokin tattalin arziki ta Najeriya ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye kudurin dokar da ya gabatarwa majalissar dokokin kasar kan sauye sauyen da suka shafi haraji.

Majalissar wadda ta kunshi daukacin gwamnonin kasar ta gabatar da wannan bukata ce ta bakin gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde lokacin da yake ganawa da manema labarai dake fadar shugaban kasa a birnin Abuja jiya Alhamis 31 ga watan jiya na Oktoba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Gwamnan ya ce, majalissar ta yi kira ga shugaban kasar da ya gaggauta janye kudurin dokar domin dai bayar da damar fadada tuntuba ta yadda za a samar da matsaya ta bai daya da kowa zai gamsu.

Taron majalissar tattalin arzikin na kasa da aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, ya ce saboda muhimmancin da dokar ke da shi da kuma sarkakiyar dokar musamman ma ga rayuwa da tattalin arzikin al’ummar kasa, akwai matukar bukata a yi wa dokar ’yan gyare-gyaren da suka kamata, kuma hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar tuntubar dukkannin bangarori.

To sai dai kuma a martanin da fadar shugaban kasa ta yi a game da bukatar taron majalissar tattalin arzikin na kasa, ta tabbatarwa ’yan Najeriya cewa, kudurin dokar da aka mikawa zauren majalissar dokokin ta kasa an tsara shi ne yadda kowacce jiha za ta amfana.

Cikin bayanin da mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin yada labarai Bayo Onanuga ya yi a wata sanarwar da ya fitar da yammacin jiya Alhamis, ya ce babu wata jiha da za a dannewa hakki ko dama kamar yadda dai kungiyar gwamnonin arewa take fargaba.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, kudurin dokokin da aka gabatar ba shi da wata nasaba da karin kudaden haraji a kasa, illa kawai sake tsarin hanyoyin karbar harajin cikin sauki ta hanyar dabarun zamani. (Garba Abdullahi Bagwai)