Koriya ta Arewa ta gwada sabon makami mai linzami na ICBM Hwasongpho-19
2024-11-01 10:58:58 CMG Hausa
Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa KCNA ya rawaito yau Juma'a cewa, Koriya ta Arewa ta gudanar da wani muhimmin gwaji na sabon makami mai linzami samfurin ICBM Hwasongpho-19 mai doguwar tafiya kirar kasar, a jiya Alhamis.
Rahoton KCNA ya ce makamin ya yi tafiyar kilomita 1,001.2 a dakika 5,156 kafin ya sauka a wani wuri da aka tsara a tekun gabashin kasar, kuma gwajin ba shi da illa ga tsaron kasashe makwabta.
Babban sakatare na jam'iyyar ma'aikata ta Koriya ta Arewa kuma shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, da kansa ya jagoranci aikin gwajin, inda ya kira gwajin "matakin sojan da ya dace" don nuna matakin da kasar za ta dauka wajen mayar da martani ga tabarbarewar yanayin tsaro da ake ciki a zirin Koriya, kuma wani bangare ne na "tsari mai mahimmanci" a ci gaba da bunkasa dabarun kai hari na kasar. (Yahaya)