Yawan wutar lantarkin da Sin ta samar ta hanyar dogaro da makamashi mai tsabta ya kai kw/h triliyan 2.51 daga watan Janairu zuwa Satumba
2024-11-01 13:55:41 CMG Hausa
A gun taron manema labarai da hukumar makamashi ta kasar Sin ta shirya a jiya Alhamis, kakakin hukumar Mr. Zhang Xing ya ce, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, yawan wutar lantarki da Sin ta samar ta hanyar dogaro da makamashi mai tsabta ya karu sosai, adadin ya kai kw/h triliyan 2.51, wanda ya karu da kashi 20.9% bisa na makamancin lokacin bara, kuma ya kai kashi 35.5% bisa na dukkan wutar lantarkin da Sin ta samar. Daga cikinsu, wutar lantarkin da aka samar ta amfani da iska da hasken rana ya kai kw/h biliyan 1349, wanda ya karu da kashi 26.3% bisa na makamancin lokacin bara, adadin ya yi daidai da wutar lantarki da masana’anta ta uku ta amfani da shi, wato sana’ar nishadi da ba da hidima da sauransu. Adadin da ya zarce yawan wutar lantarkin da jama’a ke amfani da shi yau da kullum. (Amina Xu)