logo

HAUSA

Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa wasu ’yan bindiga sun mamaye daya daga cikin cibiyoyin bayar da horon ta

2024-10-31 11:33:33 CMG Hausa

Hedikwatar tsaron Najeriya  ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa wai wasu ’yan bindiga sun mamaye sansanin horas da dakarunta dake Kontagora a jihar Niger.

Wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labaran hedikwatar tsaro ta kasa Major General Edward Buba ta yi bayanin cewa, har yanzu filin yana karkashin kulawar rundunar sojin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanarwar ta yi bayanin cewa, tun bayan bullar wannan labari, sashen binciken sirri na rundunar ya gudanar da bincike a kan al’amarin kuma ya tabbatar da cewa, babu wasu ’yan ta’adda a wannan waje, illa dai kawai wasu makiyaya ne suke gudanar da kiwon dabbobinsu.

Ya ce, ko a ’yan kwanakin nan dakarun sojin sun yi fito na fito da gungun wasu ’yan ta’adda da suke addabar wasu al’umomi a jihar ta Niger, kuma dakarun sun yi nasarar tarwatsa su, amma ko da inci daya na sansanin bayar da horon ba ya hannun ’yan ta’adda.

Major Janaral Edward Buba ya kara tabbatar da cewa, ayyukan dakarun tsaron dake jihar yana matukar tasiri gaske wajen hana ’yan ta’adda sakewa, inda ya kara shan alwashin cewa, rundunar tsaron ta kasa ba za ta taba gajiyawa ba wajen kakkabe duk wasu ’yan ta’adda a jihar ta Niger da ma sauran sassan kasa.

Ya kuma kara jaddada cewa, rundunar tsaro tana aiki tare da gwamnatin jihar Niger wajen samar da dauwamammen zaman lafiya a jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)