logo

HAUSA

Han Zheng ya gana da kakakin majalissar dokokin Zambia da shugaban babban taron MDD na 79

2024-10-31 21:06:44 CMG Hausa

A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da kakakin majalissar dokokin kasar Zambia Nelly Mutti, da kuma shugaban babban taron MDD na 79 Philemon Yang a nan birnin Beijing.

Yayin zantawarsa da madam Mutti, Han Zheng ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Zambia, karkashin kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, ta yadda za su tallafi juna a batutuwa masu nasaba da moriyar su, da manyan abubuwan da suke mayar da hankali a kan su, kana da aiwatar da sakamakon taron FOCAC da ya gabata a birnin Beijing, da inganta matsayin hadin gwiwar su ta fuskar cinikayya da zuba jari, da samar da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya da sauran fannoni. Kaza lika, da ingiza fahimta da amincewa juna, da gina al’ummar Sin da Zambia ta kut da kut mai makomar bai daya.

A nata tsokacin, madam Mutti, cewa ta yi Zambia na nacewa manufar nan ta Sin daya tak a duniya, tana kuma godewa Sin bisa tallafi mai fa’ida da ta dade tana baiwa kasar, kuma Zambia a shirye take ta ci gaba da yayata dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu, domin samar da gagarumin ci gaba.

A yayin zantawarsa da mista Yang kuwa, Han Zheng ya ce Sin na nacewa goyon baya, da ba da gudummawa mai ma’ana ga ayyukan MDD, wanda hakan jigo ne dake shaida rungumar samar da tasiri daga sassa mabanbanta. Ya ce shekara mai zuwa za a yi bikin cikar MDD shekaru 80 da kafuwa, kuma Sin ta kasance muhimmin ginshiki a ayyukan kasa da kasa da majalissar ke gudanarwa, kuma za ta ci gaba da rike matsayin ta na martaba ikon MDD, da aiki tukuru wajen tabbatar da nasarar sauye- sauye, da bunkasar tsarin gudanarwar kasa da kasa, da tabbatar da tsarin yana gudana bisa adalci da daidaito.

A nasa bangare kuwa, mista Philemon ya ce MDD za ta amince da kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD, da manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, yana mai fatan karfafa hadin kai tare da Sin, da bayar da babbar gudummawa ga aikin kare zaman lafiyar kasa da kasa, da yayata ci gaban bai daya.    (Saminu Alhassan)