Tawagar likitocin Sin ta ba da gudummawar kayayyakin aikin jinya ga asibitin Tanzaniya
2024-10-31 11:05:00 CMG Hausa
Tawagar likitocin kasar Sin karo na 27 dake Tanzaniya ta ba da gudummawar na'urorin binciken makogoro ko laryngoscope ga sashen kula da kawar da radadin aikin tiyata na asibitin kasa na Muhimbili (MNH), babbar cibiyar kula da lafiya ta kasar.
A cewar sanarwar MNH da aka fitar jiya Laraba, na'urorin da darajarsu ta kai kimanin yuan 150,000 kwatankwacin dalar Amurka 21,000, za su taimaka wa sashen kula da kawar da radadin aikin tiyata wajen sauyawa daga yin amfani da dabarun gama-gari zuwa hakikanin dabarar kula da kawar da radadin aikin tiyata.
Asibitin ya nuna godiya ga tawagar likitocin kasar Sin da suka dade suna ba da jagoranci na fasaha da taimakon likitanci, yana mai cewa, taimakon na'urar binciken makogoro ya zo kan lokaci, wanda zai inganta tsaron marasa lafiya a lokacin kawar da radadin aikin tiyata da kuma magance kalubalen da sashen ke yawan fuskanta.
Ya kara da cewa, tawagar likitocin kasar Sin za ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da tallafawa kasar Tanzaniya. (Yahaya)