Shugaban Zambabwe ya yi kira ga kasashen Afirka da su magance illar da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar al’umma
2024-10-31 09:40:55 CMG Hausa
A jiya Laraba ne shugaban kasar Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara yin bincike da sa ido don fahimtar yadda sauyin yanayi ke shafar kiwon lafiya, musamman yaduwar cututtuka da matsanancin zafi.
Mnangagwa ya bayyana hakan ne a yayin taron kasa da kasa kan yanayi da kiwon lafiya na Afirka karo na farko a Harare, babban birnin Zimbabwe, inda ya ce, ya kamata a ci gaba da gudanar da bincike kan masu rauni da suka hada da mata da yara da kuma masu bukata ta musamman. Kana ya kamata a ba da fifiko kan gano muhimman alamun sauyin yanayi masu nasaba da kiwon lafiya, da kuma inganta sa ido kan karfin tsarin kiwon lafiya don shawo kan barkewar cututtuka, saboda hakan na da muhimmanci ga gina tsarin kiwon lafiya mai jurewa yanayi. Yana mai cewa, yana fatan bayanan da aka gabatar a taron za su yi tasiri a duk fadin Afirka, kuma za su zama tushen gudunmawar da nahiyar za ta bayar a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na shekarar 2024. (Yahaya)