logo

HAUSA

Sama da 'yan Najeriya miliyan 33.9 ne ba sa cikin tsarin hada-hadar kudi

2024-10-31 10:23:52 CMG Hausa

Babban bankin Najeriya wato CBN, ya bayyana jiya Laraba cewa, a kalla mutane miliyan 33.9 ne ba sa cikin tsarin hada-hadar kudi na banki.

Mukaddashin shugaban sashen kula da kariyar masu sayayya na babban bankin, Ibrahim Yahaya ne bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a gefen wani shiri da aka gudanar domin murnar zagayowar ranar ajiye kudi a banki ta duniya ta shekarar 2024 a Abuja, babban birnin tarayya, yana mai cewa, babban bankin ya samu ci gaba a adadin mutanen da ke cikin tsarin hada-hadar kudi na banki, inda ‘yan Najeriya miliyan 54.2 ke da asusun ajiyar kudi a banki a shekarar 2023.

Ya kuma ce, kimanin kashi 32 cikin 100, ko kuma mutane miliyan 33.9, ba sa cikin tsarin hada-hadar kudi na banki gaba daya, Yana mai kira   da a rumgumi al’adar ajiye kudi a banki, musamman matasa, inda ya ce kudaden da ake ajiyarsu a banki na karuwa.

Ya kara da cewa, CBN ya gano cewa, ajiye kudi a banki na da karin fa’ida ga tattalin arziki, saboda yana taimaka wa bankuna wajen ba da lamuni mai ma’ana ga sassan masana’antu, wanda ke haifar da ci gaban tattalin arziki. (Yahaya)