Shugaba Xi ya sanya hannu kan kundin ka’idojin inganta lura da fannin dakarun ko ta kwana
2024-10-31 20:55:13 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya hannu kan kundin ka’idojin inganta lura da fannin dakarun soji na ko ta kwana a ’yan kwanakin da suka wuce. Manufar samar da ka’idojin, ita ce ingiza aiwatar da dokar kasar Sin mai nasaba da dakarun ko ta kwana.
Kaza lika, ka’idojin za su mayar da hankali ga kafa wani managarcin tsarin lura da dakarun a sabon zamani, da cikakken tsarin zabar su, da mukaman su, da ayyukan da za su iya shiga, da horaswa, da tantance kwazon su, da moriyarsu da tsarin ritayar su.
A matsayin muhimmin sakamako na sauye-sauye a fannin samar da dakarun sojin kasar Sin, tabbatar da wannan ka’idoji zai zama muhimmin jigo na doka, daidaitaccen tsari, mai dacewa da kimiyya a bangaren samar da dakarun ko ta kwana masu kwarewa da sanin makamar aiki.
(Saminu Alhassan)