logo

HAUSA

Sake amfani da ciyayin alkama ko na shinkafa a kasar Sin ya sa bola ta zama jari

2024-10-31 13:48:39 CMG Hausa

Manoma a duk fadin kasar Sin na himmatuwa wajen girbin amfanin gona, inda kuma ake yawan samun ciyayin alkama ko na shinkafa bayan girbi. Amma manoman kasar Sin sun bullo da wasu sabbin dabaru ko hanyoyi na sarrafa ciyayin gonaki, don bola ta zama jari mai daraja, al’amarin da ya sa manoma suka kara samun kudin shiga, yayin da kuma muhallin halittu ya kara kyautata.