Shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP ya karbi wata tawagar kasar Chadi a birnin Yamai
2024-10-30 10:11:37 CMG Hausa
A ranar jiya Talata, 29 ga watan Oktoban, shugaban kasar Nijar, kana shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, Abdourahamane Tiani ya karbi wata tawagar Chadi dake karkashin Abderahman Koulamallah, ministan harkokin wajen Chadi, kuma manzon musamman na shugaba Mahamat Idriss Deby Itno.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A lokacin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida jim kadan, bayan ganawa tare da shugaban kasar Nijar Abdrourahamane Tiani, ministan harkokin wajen kasar Chadi ya bayyana cewa, ya zo Yamai dauke da wani sako na shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, da ya kamata da kansa ya yi wannan ziyara, amma hakan bai samu ba, dalilin al’amarin da kasar ta fuskanta tare da harin ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, shugaba ya dora mini wannan nauyi na kawo wannan sako na godiya, da zumunta, da goyon baya ga shugaban kasa, ga gwamnatin Nijar da kuma al’ummar Nijar, ganin cikin halin da Nijar take ciki, da kuma hanyar da ta dosa ta neman cin gashin kai da kuma ’yanci ta hanyar sake gina kasa.
A yayin wannan tattaunawa, shugaban diplomasiyyar Chadi ya tabo batutuwa da dama tare da shugaban kasar Nijar, musamman batutuwa tsaro, domin suna a sahun gaban tattaunawa da karfafa huldar dangantakarmu, in ji ministan harkokin wajen Chadi.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.