An yi bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Zambia
2024-10-30 10:26:35 CMG Hausa
A jiya Talata ne kasashen Sin da Zambia suka gudanar da bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
An gudanar da bikin ne a wurin shakatawa na tunawa da TAZARA da ke gundumar Chongwa mai nisan kilimita 39 gabas da Lusaka, babban birnin Zambia. Kana an ajiye furanni don girmama Sinawa da suka mutu yayin aikin layin dogo na Tanzaniya zuwa Zambia wato layin TAZARA.
Bikin wanda aka gudanar a karkashin taken “Ku mika ruhin TAZARA ga zamani mai zuwa da gina makomar bai daya tare” ya samu halartar jakadan kasar Sin a Zambia Han Jing, da shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema, da jami'ai daga ofishin jakadancin kasar Sin da gwamnatin Zambia. (Mai Fassara : Mohammed Yahaya)