Wakiliin Sin ya yi kira ga Amurka da ta dage takunkumin da ta kakabawa Cuba
2024-10-30 11:25:20 CMG Hausa
A ranar 29 ga watan Oktoba, agogon kasar, wakilin Sin ya yi kira ga Amurka da ta dage takunkumin da ta kakakbawa Cuba, a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da ya gudana kan batun “Bukatar kawo karshen takunkumin tattalin arziki, cinikayya da hada-hadar kudi da Amurka ta kakakbawa Cuba”.
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana cewa, yanzu sama da shekaru 60 ke nan da Amurka ta sanya cikakken takunkumi kan kasar Cuba, lamarin da ya jawo asarar daruruwan biliyoyin daloli ga kasar Cuba, tare da haddasa mummunan bala’in jin kai. Irin wannan dabi'a ta danniya da mamaya, babu makawa kasashen duniya za su yi Allah-wadai da ita. Kana kasar Sin ta sake yin kira da kakkausar murya ga Amurka da ta gaggauta janye takunkumin da ta kakabawa kasar Cuba bisa manufa da ka'idojin yarjejeniyar MDD da kuma ka'idojin dokokin kasa da kasa. (Yahaya)