CMSA: An yi nasarar harba kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati
2024-10-30 10:25:44 CMG Hausa
Hukumar kula da ’yan sama jannati na kasar Sin ko CMSA ta ce an yi nasarar harba kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati.
A ranar Laraba ne kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati, inda ta aika da ’yan sama jannati uku, ciki har da mace injiniyan sararin samaniya ta farko ta kasar, zuwa falakinsa a tashar sararin samaniya don gudanar da aikin watanni shida.
CMSA ta ce, kumbon wanda aka dora a jikin rokar Long March-2F, ya cilla sama ne da misalin karfe 4 da minti 27 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. Kana, kimanin mintuna 10 da harbawa, kumbon Shenzhou-19 ya rabu da rokar, kuma ya shiga falakinsa kamar yadda aka tsara, a cewar CMSA. (Mohammed Yahaya)