Sin ta ki amincewa da sakamakon binciken da EU ta gabatar kan batun motoci masu aiki da wutar da lantarki kirar Sin
2024-10-30 10:18:43 CMG Hausa
Yau Laraba, ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta mai da martani ga sakamakon binciken da EU ta gabatar dangane da motoci masu aiki da wutar lantarki kirar Sin, inda ta ce, matakan da EU ta dauka a cikin binciken sun sabawa gaskiya da ka’idoji, saboda haka Sin ba ta yarda da sakamakon ba ko kadan, kuma ta riga ta kai kara ga tsarin daidaita bambancin ra’ayi na WTO.
An rawaito cewa, ran 29 ga watan nan da muke ciki agogon Jamus, shugabar kungiyar motoci ta kasar Jamus Hildegard Müller ta gabatar da wata sanarwa cewa, koma bayan cinikayya cikin ‘yanci ne duba da karin harajin da EU ke shirin bugawa irin wadannan motoci, kuma matakin ya yi mummunan tasiri ga yunkuirin tabbatar da wadata, da samar da guraben aikin yi, da bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar Turai.
A wannan rana da safe, kwamitin EU ya ba da labarin yanke shawarar bugawa motoci kirar Sin da za su shiga kasashen Turai karin haraji a shekaru 5 masu zuwa. (Amina Xu)