’Yan sama jannati dake cikin kumbon Shenzhou-19 sun yi nasarar shiga tashar sararin samaniya
2024-10-30 14:09:38 CMG Hausa
Hukumar kula da ’yan sama jannati ta kasar Sin ta sanar da cewa, kumbon Shenzhou-19 mai dakon ’yan sama jannati 3 na kasar Sin ya yi nasarar hade da tashar sararin samaniya a yau Laraba.
Kumbon ya yi kewaye-kewayen da ka tsara kuma ya sauka a gaban tashar sararin samaniya ta Tianhe da misalin karfe 11 na safe agogon Beijing.
’Yan sama jannatin guda uku dake cikin kumbon daga bisani sun shiga cikin na’urar Tianhe inda suka hadu da ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18 dake jiran isowarsu. (Yahaya)