Ya Kamata Kowace Kasa Ta Ba Da Muhimmanci Kan Samar Da Amfanin Gona
2024-10-30 07:22:03 CGTN Hausa
Noma na daya daga cikin mafi dadewa kuma mafi muhimmanci aiki na dan Adam, domin tana samar da kayan masarufi na rayuwa da walwala. Kuma noma na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki, Noma na tallafawa ci gaban zamantakewar al'umma ta hanyar inganta rayuwa, ilimi da lafiyar al'ummomin karkara. Har ila yau noma na samar da hadin kan jama'a, da daidaita bambancin al'adu da daidaiton jinsi. Noma na iya rage kaura zuwa birane, da rage yunwa da rashin abinci mai gina jiki, da karfafa mata da matasa. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, noma mai dorewa na daya daga cikin muhimman manufofin kawo karshen yunwa, da samun wadatar abinci da inganta abinci mai gina jiki da kuma samar da ci gaba mai dorewa. Kuma bisa wannan dalilin ne "Ya kamata kowace kasa ta ba da muhimmanci kan samar da amfanin gona".
A watan Disamba na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a babban taron ayyukan raya karkara na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda ya bayyana cewa, "Kasar Sin ba za ta iya barin ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, a fannin noman hatsi, ya sa, ta gafala game da tabbatar da wadatar abinci a kasar ba. Kada mu manta da irin wahalhalun da yunwa ta saka mu a baya don kawai mun samu murmurewa. Maimakon haka, ya kamata mu gane cewa batun samar da abinci jar layi ne wanda zai haifar da mummunan sakamako idan har muka yi watsi da shi. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)