logo

HAUSA

’Yan ta’adda sun mamaye wani sansanin bayar da horo na sojoji a jihar Niger ta Najeriya

2024-10-30 10:10:17 CMG Hausa

Majalissar dokokin jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya tana karar da gwamnatin tarayyar cewa, wasu gungun ’yan ta’adda sun mamaye sansanin horas da sojoji dake Nagwamase a yankin karamar hukumar Kontagora.

Dan majalissa mai wakiltar yankin a majalissr dokokin jihar Alhaji Abdullahi Isah ne ya tabbatar da hakan yayin zaman majalissar na jiya Talata 29 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake gabatar da kudurin bukatar gaggawa yayin zaman majalissar, Alhaji Abdullahi Isah ya ce, filin sansanin horas da sojojin yana da girman gaske inda ya tashi tun daga karamar hukumar Kontagora ya hade da wani yankin na karamar hukumar Mariga, amma abin takaici yanzu haka ’yan ta’adda sun mayar da shi matsuguninsu.

Haka kuma dan majalissar ya ci gaba da cewa, ’yan ta’addan sun kori a kalla al’umomi 23 daga gonakinsu wanda ke makwaftaka da sansanin horas da sojojin.

Ya ce, kamar yadda bincike ya nuna ’yan ta’addan sun samar da kananan sansanoni har guda 8 a cikin filin mallakin rundunar soji ta kasa.

Hon Abdullahi Isah ya shaidawa zauren majalissar cewa, kasancewar ’yan ta’addar a wannan waje babban kalubale ne ga yanayin tsaro a yankunan kananan hukumomin Kontagora da Mariga.

Bayan doguwar muhawara da ’yan majalissar suka gudanar, sun bukaci gwamnatin jihar ta Niger da ta hanzartar hada kai da hukumar rundunar soji ta kasa domin fatattakar wadannan ’yan ta’adda da suka yi sansani a filin horas da dakarun soji na kasa, don tabbatar da ganin cewa al’ummomin dake yankin sun koma gonaki da kuma muhallansu. (Garba Abdullahi Bagwai)