logo

HAUSA

EU za ta janyowa kan ta lahani sakamakon kakaba karin haraji kan motoci masu aiki da lantarki kirar Sin

2024-10-30 21:50:49 CMG Hausa

Ba tare da yin la’akari da adawa daga bangarori daban daban ba, hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai EU, ta yanke hukuncin kakaba karin haraji kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin a jiya Talata. Game da wannan mataki, bangaren kasar Sin ya tabbatar da cewa, ba zai amince ba, kuma ba zai karba ba, kuma ya riga ya kai kara a karkashin tsarin sasanta gardama na WTO.

Me ya sa kasar Sin “ba ta amince da kuma karba ba”? Saboda ayyuka daban-daban na bangaren Turai “ba su dace ba kuma ba sa kan doka”. Wato EU na fakewa da sunan “Takara ta adalci” da yin kariyar ciniki, matakin da zai gurgunta tsarin hadin gwiwar samar da hajoji tsakanin Sin da EU, kana zai illata moriyar masu sayayya na kasashen Turai, tare da illata muhallin zuba jarin na EU, da ma burin da kasashe mambobin EU ke da shi na sauya alkibla zuwa amfani da makamashi maras gurbata muhalli. Wanda hakan ya kasance matakin da zai janyowa sauran kasashe da ma kanta lahani.

A matsayinta na kungiyar tattalin arziki ta shiyya-shiyya mafi girma a duniya, an danganta nasarar da kungiyar ta EU ta samu a baya ga yin ciniki cikin ’yanci, sannan kuma za ta dogara da hakan don kara samun ci gaba a nan gaba. Ya dace ta saurari muryoyin cikin kungiyar, da ainihin bukatun kamfanoni, wato “Ba ma bukatar sanya karin haraji ba, muna bukatar ka’ idojin ciniki masu adalci.” (Bilkisu Xin)