Horor da kasar Sin take tallafawa ya inganta yaki da nakiyoyin da aka binne a Somaliya
2024-10-30 10:27:19 CMG Hausa
A jiya Talata ne hukumar kula da ababen fashewa ta Somaliya ko SEMA, ta kaddamar da wani shirin ba da horo na kwanaki uku don inganta iya aiki, wanda ke mai da hankali kan inganta harkokin gudanarwa da kula da ma’aikata don karfafa yaki da na’urori masu fashewa.
Ofishin jakadancin Sin dake Somaliya ne ya dauki nauyin wannan shirin, wanda ke kokarin inganta aikin hukumar ta SEMA, a fannonin da suka shafi muhimman ayyukan nakiyoyi da kawar da ragowar ababen fashewa na yaki (ERW).
A jawabinsa na bude taron, babban daraktan hukumar SEMA, Dahir Abdirahman Abdulle, ya nuna jin dadinsa ga yadda kasar Sin ke ci gaba da ba da taimako wajen karfafa ayyukan hukumar. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)