logo

HAUSA

Sin ta zargi EU da bayar da kariyar cinikayya bayan da kungiyar ta kakaba karin haraji kan motoci masu aiki da lantarki kirar Sin

2024-10-30 20:10:45 CMG Hausa

A jiya Talata ne hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar turai EU, ta sanar da kammala binciken karshe, tare da yanke hukuncin kakaba karin haraji kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin.

Game da wannan mataki, yayin taron manema labarai na Larabar nan, kakakin ma’aikatar harkokin waje ta Sin Lin Jian, ya ce hukumar EU ta dage sai ta gudanar da bincike ba tare da dalili ba, ta kuma kakabawa motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin haraji, ba tare da tuntubar masana’antun da abun ya shafa ba, wanda ko shakka babu matakin ba komai ba ne illa baiwa kamfanonin Turai kariyar cinikayya.

Lin Jian, ya kara da cewa, matakin EU zai gurgunta tsarin hadin gwiwar raya samar da hajoji, da shigar da su sassa daban daban tsakanin Sin da EU, kana zai illata moriyar masu sayayya na kasashen turai, da ma burin da kasashe mambobin EU ke da shi na sauya alkibla zuwa amfani da makamashi maras gurbata muhalli, da kokarin da duniya ke yi na magance kalubalen sauyin yanayi.

Bugu da kari, Lin Jian ya yi tsokaci kan ci gaba da farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, inda ya ce Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakai daidai da zaton al’ummun kasa da kasa, tare da bude sabbin babuka, da damammakin bunkasa tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)