Yawan kudin shigar kamfanonin al’adu masu karfi a Sin ya karu da 5.9% daga watan Janairu zuwa na Satumban bana
2024-10-30 10:54:23 CMG Hausa
Bisa binciken da aka yi kan kamfanonin al’adu masu karfi dubu 78 a nan kasar Sin, an ce, daga watan Janairu zuwa na Satumba na bana, yawan kudin shigar wadannan kamfanoni ya kai kimanin dalar triliyan 1.4, wanda ya karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, kananan nau’o’in sana’a guda 16 dake bayyana sabbin halayen musamma a bangren al’adu, yawan kudin shigarsu ya kai fiye da dalar biliyan 583, wanda ya karu da kashi 10% bisa na makamancin lokaci.
A bangaren matsakaicin girman nau’o’in sana’a kuwa, ba da hidimar yanar gizo da dandalolin nishadi da dai sauransu sun ba da jagoranci a bangaren samun kudin shiga. (Amina Xu)