Shugaban babban taron MDD karo na 79 zai ziyarci kasar Sin
2024-10-30 19:36:35 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya sanar a Larabar nan cewa, shugaban babban taron MDD karo na 79 mista Philemon Yang, zai ziyarci kasar Sin tsakanin yau Laraba zuwa Lahadi 3 ga watan Nuwamba dake tafe, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen Sin, kana mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS Wang Yi ya yi masa. (Saminu Alhassan)