Sojojin Chadi 40 sun mutu a cikin wani harin kungiyar Boko Haram
2024-10-29 13:36:31 CMG Hausa
Cikin daren Lahadi 27 zuwa Litinin 28 ga watan Oktoban shekarar 2024, kungiyar Boko Haram ta kai wani kazamin hari kan sojojin kasar Chadi kusa da tafkin Chadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji kusan 40 daga cikinsu har da wani kwamandan din wata bataliya.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Gaban wannan kazamin hari, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, da kansa ya kai rangadi wurin da lamarin ya abku, domin sanya ido kan aikin mai da martani, kuma ya sanar da wani aikin kakkaba mai taken Haskanite, dake da burin farautar wadannan mahara a duk inda suka shiga.
A cewar majiyoyin soja, harin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a wani barikin sojojin Chadi da ke Barkaram a cikin jihar Kaya, mai tazarar kimanin kilomita 10 daga iyaka da tarayyar Najeriya.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.