logo

HAUSA

Shahararren darektan fim daga Nijar Laouali Gazali: Ziyarata a kasar Sin ta bude mini idanu sosai!

2024-10-29 15:23:57 CMG Hausa

Kwanan ne shahararren matashin darektan shirya fina-finai daga Jamhuriyar Nijar malam Laouali Gazali, ya jagoranci wata tawagar daukar fim zuwa kasar Sin, musamman birnin Beijing, da jihar Xinjiang, don gudanar da ayyukan daukar fina-finai bisa hadin-gwiwa da sashin Hausa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice.

Kafin kammala ayyukansu a kasar Sin, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Laouali Gazali ta waya, inda ya yi karin haske game da abubuwan da suka burge shi a wurare daban-daban na kasar Sin, da ainihin abubuwan da ya gani da idanunsa a kasar.

Ya kuma yi kira ga mutanen nahiyar Afirka, da kada su yi saurin yarda da labaran karya da kafafen watsa labaran kasashen yammacin duniya suke yadawa game da kasar Sin, saboda gani ya kori ji. (Murtala Zhang)