Guterres ya yi kira da a dauki matakan dakatar da tashe tashen hankula da kare fararen hula a Sudan
2024-10-29 09:22:22 CMG Hausa
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a yi azamar daukar matakan dakatar da tashe tashen hankula, da kare fararen hula a kasar Sudan mai fama da yaki, duk da cewa kawo yanzu babu halin tura dakarun MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya zuwa kasar.
Guterres, ya yi kiran ne cikin tsokacin da ya yi a zaman kwamitin tsaron MDD, game da halin da ake ciki a kasar ta Sudan a jiya Litinin. Ya ce kawo yanzu, an shiga wata na 18 ana dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin kasar da dakarun RSF, kuma a kullum al’ummar kasar na kara tsunduma cikin mawuyacin hali, yayin da yaki ya jefa kusan mutane miliyan 25 cikin bukatar tallafi.
Mista Guterres ya kara da cewa, abubuwa 3 mafiya muhimmanci game da kare fararen hular Sudan su ne gaggauta dakatar da bude wuta, da kare rayukan fararen hula, da kuma samar da zarafin shigar da tallafin jin kai cikin kasar.
Daga nan sai ya ja hankalin majalissar da ta ci gaba da goyon bayan jakadansa na musamman a Sudan mista Ramtane Lamamra, a kokarinsa na kawo karshen rikicin kasar, kana a ingiza sahihan matakai na tattaunawa da sauran hukumomin shiyyar, kamar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da kungiyar bunkasa yankin gabashin Afirka ta IGAD, da kungiyar tarayyar Larabawa ta LA da dai sauran su. (Saminu Alhassan)