Sin ta yi kira da a yi hakuri da juna tare da nuna adawa da keta zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
2024-10-29 11:59:54 CMG Hausa
Game da harin da Isra’ila ta kaiwa kasar Iran a ran 26 ga watan nan da muke ciki, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya bayyana a gun taron gaggawa da kwamitin sulhu na majalisar ya gudanar, kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya a jiya Litinin cewa, Sin ta yi tir da ko wane irin matakin da ake dauka, ko za a dauka dake keta cikakken ikon mallakar yankunan kasar Iran, kuma tana adawa da kawo cikas ga zaman lafiya, da kwanciyar hankalin a yankin.
Fu Cong ya kuma yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su yi hakuri da juna, da komawa hanyar da ta dace ta warware rikici ta hanyar siyasa da diflomasiyya.
Fu ya kara da cewa, halin da yankin ke ciki na kara kamari, tushen hakan kuma shi ne gaza cimma matsaya daya game da dakatar da bude wuta a zirin Gaza. Don haka kasar Sin ta yi kira ga Isar’ila da dai sauran kasashe masu karfi, da su dauki ceton rayukan mutane da muhimmanci, da ma yin watsi da makarkashiyar siyasa, da goyon bayan kwamitin, wajen daukar karin matakai game da yanayin da ake ciki yanzu, da ma gaggauta dakatar da bude wuta a Gaza, kana da kara azamar kwantar da hankali tsakanin Lebanon da Isra’ila, don hana yaduwar rikicin zuwa sauran wurare. (Amina Xu)