Kasar Sin ta yi tir da dokokin Amurka na dakile zuba jari a sassan fasaha na Sin
2024-10-29 19:51:29 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Talata cewa, kasar Sin ta nuna rashin gamsuwa da yin adawa da kakkausar murya ga sanarwar da Amurka ta yi na dokokin kayyade zuba jari saboda kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar Lin Jian ya ce, kasar Sin ta bayyana ra’ayinta ga Amurka, kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye halaltattun hakkokinta da moriyarta.
A lokacin da yake amsa tambayar dan jarida game da rattaba hannu kan yarjejeniyar da Taiwan ta kulla da gwamnatin Amurka don sayen jiragen sama marasa matuka daga kamfanoni biyu, Lin Jian ya ce Taiwan lardi ne na kasar Sin, kuma babu “ma’aikatar tsaro” a Taiwan. Matsayin da kasar Sin ta dauka na nuna adawa da huldar soji tsakanin Amurka da Taiwan a bayyane yake. Kuma kasar Sin ta kakabawa kamfanonin biyu na Amurka da abin ya shafa takunkumi. (Yahaya)