Sin za ta harba kumbon “Shenzhou-19” mai daukar ’yan sama jannati 3
2024-10-29 11:48:02 CMG Hausa
An gudanar da taron manema labarai, don gane da shirin harba kumbon “Shenzhou-19”, mai daukar ’yan sama jannati 3 da safiyar yau Talata. Yayin taron, mai magana da yawunsa ya ce, Sin za ta harba kumbo “Shenzhou-19” a gobe Laraba 30 ga watan nan, da karfe 4 da mintuna 27 na asuba, bisa shawara daga babbar cibiyar ba da jagorancin aikin.
Wani rahoto daga ofis mai kula da ayyukan kumbuna masu daukar ’yan sama jannati, ya ce babbar cibiyar ba da jagoranci kan nazarin raya tashar sararin samaniya da ayyukan zirga-zirgar kumbuna ta Sin, ta yanke shawara ce bayan nazari.
Kaza lika, 'yan sama jannati 3, wato Mr. Cai Xuzhe, da Mr. Song Lingdong, da madam Wang Haoze, za su kasance cikin kumbo na “Shenzhou-19” bisa jagorancin Cai Xuzhe, wanda zai kasance mai ba da umurni. (Amina Xu)