A kalla sojojin Chadi 40 sun rasu sakamakon wani hari kan sansanin soji na Barkaram
2024-10-29 09:42:24 CMG Hausa
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar Chadi, ta ce sojojin kasar 40 dake aiki a sansanin tsibirin Barkaram na lardin Lac sun rasa rayukan su, yayin wani farmaki da aka kai musu a ranar Lahadin karshen makon jiya.
Sanarwar ta ce shugaban kasar Mahamat Idriss Deby Itno, ya ziyarci sansanin a jiya Litinin, domin nuna alhinin rasuwar sojojin, tare da jajantawa wadanda suka jikkata.
Kaza lika, shugaban na Chadi ya kaddamar da aikin farautar wadanda suka aikata wannan ta’asa, ko da yake gwamnati ba ta bayyana ainihin wadanda ake zargi da kai farmakin sansanin sojojin ba.
To sai dai kuma duk da hakan, kafofin watsa labarai na cikin kasar sun dora alhakin harin kan mayakan kungiyar Boko Haram, wadanda ke yawan kaddamar da hare hare a yankin tafkin Chadi. (Saminu Alhassan)