Shugaban tarayyar Najeriya ya bayar da umarnin a gaggauta dawo da wutan lantarki a arewacin kasar
2024-10-29 13:35:29 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a hanzartar maido da wutan lantarki a wasu jihohin arewa 17 na kasar bayan shafi kusan mako biyu a lalace, lamarin da ya sanya al’ummar shiyyar zama cikin duhu.
Shugaban ya bayar da umarnin ne jiya Litinin 28 ga wata a birnin Abuja cikin wata sanarwar da mashawarcin sa kan harkokin yada labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga ya rabawa manema labarai.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Matsalar rashin wutar dai ta samo asali ne daga lalacewar babban layin dakon wuta daga Shiroro sakamakon harin ’yan bindiga.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana shugaban na tarayyar Najeriya ya nuna bakin cikinsa bisa faruwar wannan al’amari wanda ya haifar da zaman kunchi ga al’umomin dake shiyyar arewacin Najeriya.
Wannan ya sanya shugaban gayyato ministan lura da harkokin wuta na kasar Mr Adebayo Adelabo da mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro Nuhu Ribadu domin hada karfi waje guda don tabbatar da ganin cewa an shawo kan matsalar da ta sukurkutar da yanayin rayuwa da na tattalin arzikin shiyyar.
Bayan kammala ganawar da shugaban kasar ne, ministan harkokin wutan lantarki Mr Adebayo Adelabo yake shaidawa manema labarai cewa tuni aka fara aikin gyara kayayyakin da aka lalata a layin da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna, kuma za a kammala nan da kwanaki 5. (Garba Abdullahi Bagwai)