Xi Jinping ya taya sarkin Cambodia murnar cika shekaru 20 da kasancewa a karagar mulki
2024-10-29 11:54:38 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya sarkin Cambodia Norodom Sihamoni murnar cika shekaru 20 da kasancewa a kan karagar mulki.
Xi ya ce, bayan sarki ya kama aiki, ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da karkon kasarsa, da raya tattalin arzikin kasar, da kara inganta mu’ammala tsakanin Cambodia da sauran kasashe. Ya kuma dade yana dukufa kan kara dankon zumuncin kasarsa da Sin. Hakan ya sa aka kai ga raya kyakkyawar makomar al’ummun kasashen biyu ta bai daya mai inganci a matsayin koli a sabon zamani, inda kuma aka kara zurfafa tsarin hadin gwiwa a manyan bangarori 6, wato siyasa, da karfin samar da kayayyaki, da aikin gona, da makamashi, da tsaro, kana da raya al’adu.
Kaza lika, shekarar cudanyar al’adun kasashen biyu ta kawowa al’ummun kasashe biyu alfanu mai yakini. Xi ya kuma jadadda cewa, yana mai da muhimmanci matuka kan bunkasuwar huldar kasashen biyu, yana kuma daukar dadadden zumuncin kasashen biyu da muhimmanci, tare da fatan kara hadin gwiwarsa da sarkin, don jagorantar bunkasuwar huldarsu, da ma gaggauta samun karin ci gaba wajen kafa kyakkyawar makomar al’umommin kasashen biyu ta bai daya. (Amina Xu)