Mutane 7 sun rasu sakamakon ruftawar wani gini a Abuja na Najeriya
2024-10-29 09:34:50 CMG Hausa
A kalla mutane 7 ne suka rasu, kana wasu biyu suka jikkata, yayin da wani gini da aka fara rushewa ya rufta kan wasu da ake zaton ‘yan bola jari ne dake kokarin cire roduka dake sassan ginin, a unguwar Sabon-Lugbe ta wajen birnin Abuja fadar mulkin Najeriya.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin, shugaban sashen ayyukan gaggawa na hukumar babban birnin tarayyar Najeriyar Abdulrahman Mohammed, ya ce kafin aukuwar ibtila’in, mahukuntan birnin sun fara rushe ginin, daga bisani ne kuma a ranar Asabar wasu mutane da ake zaton ‘yan gwangwan ne suka shiga suna kokarin zare rodukan dake sassan ginin, wanda hakan ya sabbaba ginin a kan su, kuma nan take aka samu asarar rayuka.
Jami’in ya ce baya ga gawawwakin mutane 7 da aka zakulo, an kuma garzaya da karin wasu mutanen biyu zuwa asibiti bayan an yi nasarar ceto su da rai. (Saminu Alhassan)