Jami’an kiwon lafiya na Mozambique sun koma gida bayan halartar horon samun kwarewa a kasar Sin
2024-10-28 13:35:44 CMG Hausa
Jami’an kiwon lafiya 14 daga kasar Mozambique sun koma gida bayan halartar horon samun kwarewa a kasar Sin. Jami’an wadanda ke aiki a babban asibitin birnin Maputo, fadar mulkin kasar ta Mozambique, sun kammala samun horon ne a birnin Chengdu, fadar mulkin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
An gudanar da horon tsakanin ranakun 5 zuwa 25 ga watan Satumban da ya shude, karkashin shirin cibiyar musayar kasa da kasa ta hukumar kiwon lafiya ta lardin Sichuan, wanda ya mayar da hankali ga dabarun ayyukan jinyar marasa lafiya, musamman fasahohin ba da agajin gaggawa ga marasa lafiya, da lura da wadanda ke cikin matsanancin yanayi, da sabbin fasahohin gudanar da tiyata mai karancin hadari ga marasa lafiya.
Horon dai bangare ne na yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Mozambique, da nufin yada ilimi, da musayar fasahohin kiwon lafiya tsakanin kwararrun jami’an kiwon lafiya na asibitin al’umma na lardin Sichuan da gamayyar kasashe masu magana da yaren Portuguese ko CPLP a takaice.
Kazalika, horon ya samu halartar karin jami’an kiwon lafiya daga kasashen Cape Verde, da Sao Tome da Principe, da Guinea-Bissau, wanda hakan ya shaida aniyar kasar Sin ta karfafa harkar kiwon kafiya a matakin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)