Kungiyar tseren keke ta duniya UCI ta hukunta kewayen tseren keke na Faso
2024-10-28 19:40:09 CMG Hausa
A kasar Burkina Faso, gasar tseren keke ta kasa da kasa, da ake kira kewayen tseren keke na Faso na gudana, a ranar jiya 27 ga watan Oktoban shekarar 2024 ne, kungiyar tseren keke ta duniya UCI ta dauki matakin hukunta kasar Burkina Faso, bisa dalilin gayyatar ‘yan wasan tseren keke CSKA Moscou na Rasha.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
An kaddamar da gasar “Tour Cycliste du Faso” wato kewayen keke na Faso, karo na 35 daga ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2024 zuwa ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2024. A tsawon kwanaki 10 masu tseren keke za su fafata bisa kilomita 1225, tare da ratsa yankuna 10.
A cewar Ignace Amedee Berewoudougou, shugaban kungiyar tseren keke ta Burkina Faso, bisa kungiyoyi 15 aka yi dakon halartarsu, saidai kungiyoyi 11 kadai suka amsa kira da ke wakiltar kasashen Belgium, Benin, Kamaru, Ghana, Holland, Mali, Morroco, Rasha da kuma Burkina Faso mai masaukin baki.
Duk da cewa, kasashen Cote d’Ivoire, Nijar, Najeriya da Senegal sun tabbatar da halartarsu, amma daga karshe ba su amsa kira ba.
Saidai, halartar ‘yan tseren keke na CSKA Moscou na Rasha a wannan gasa, kungiyar tseren keke ta duniya ta bukaci Burkina Faso da ta janye Rasha daga wannan gasa, bukatar da kasar kaftin Ibrahim Traore ta yi watsi da ita.
A ranar jiya kuma, kungiyar UCI ta bayyana cewa masu shirya Tour du Faso, sun sabawa kundin UCI, don haka ta soke wannan gasar tseren keke daga cikin ajandarta ta kasa kasa, kuma za ta dauki wasu matakan ladabtarwa kan Burkina Faso.
A nasa bangare, Joseph Pooda, sakataren dindindin na kewayen keke na Faso, ya bayyana cewa an dauki dukan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kariyar mahalarta.