Hare-haren Isra’ila kan yankunan Lebanon sun hallaka mutane 2,672 tare da jikkata wasu 12,468
2024-10-28 13:37:00 CMG Hausa
Ma’aikatar lafiya a kasar Lebanon, ta ce hare-haren da sojojin Isra’ila suka rika kaddamarwa tun daga ranar 8 ga watan Oktoban nan kan yankuna daban daban na Lebanon, sun hallaka mutane 2,672, baya ga wasu 12,468 da suka jakkata.
Kaza lika, rahotanni daga ma’aikatar lafiyar kasar sun ce a ranar Asabar kadai, adadin mutanen da hare-haren suka hallaka ya kai 19, yayin da wasu 108 suka jikkata.
Har ila yau, wasu majiyoyin jami’an gwamnati da na rundunar sojoji sun ce, a jiya Lahadi ma, irin wadannan hare-hare ta sama kan yankunan kudancin Lebanon, sun hallaka mutane 11 ciki har da wani jami’in tsaron kungiyar Hezbollah, baya ga wasu mutane 25 da suka ji raunuka.
Wata majiya ta sojoji wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewar wani jirgi maras matuki na Isra’ila ya kaddamar da hare-haren makamai masu linzami 2 ta sama, kan wani ginin dake yankin Saida na birnin Sidon, wanda ya haddasa kisan wani jami’in kungiyar Hezbollah mai suna Hussein Fneish, da iyalan gidansa mutum 7, baya ga wasu mutane 25 da suka jikkata.
A wani harin na daban kuma, sojojin Isra’ila sun tarwatsa cibiyar ba da jinya ta kungiyar Al Risala, inda suka hallaka jami’an kula da marasa lafiya 3. Da kuma wannan adadi, ma’aikatan jinya da hare-haren Isra’ila suka hallaka ya kai 167, kamar dai yadda hukumar kiwon lafiyar Lebanon din ta tabbatar. (Saminu Alhassan)