logo

HAUSA

Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5 a jihar Adamawa

2024-10-28 09:29:45 CMG Hausa

Mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da kuma aka yi asarar kaddarori da dama a wani rikici da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a yankin karamar hukumar Song dake jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Rikicin dai ya fara ne tun daga ranar Asabar 26 ga wata har zuwa safiyar jiya Lahadi 27 ga wata, inda mutane da dama kuma suka samu munanan raunuka.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

An dai sami fito na fito ne tsakanin wadannan al’umomin biyu a garin Kukta dake yankin gundumar Waltandi a karamar hukumar Song, kuma gidaje da dama ne aka kona bayan da kuma aka lalata kayayyaki masu yawan gaske.

Kamar dai yadda kakakin rundunar ’yan sandan jihar Adamawa SP Sulaiman Nguroje ya shaidawa manema labarai cikin wata sanarwar da ya fitar da yammacin jiya Lahadi ya ce, tuni dai aka shawo kan rikicin kuma rundunar ’yan sandan jihar ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu wajen kitsa rikicin.

Kakakin rundunar ’yan sandan ya tabbatar da cewa, hakika an sami asarar rayuka da kaddarori, amma dai ba a kai ga kammala tantance adadin asarar da aka yi ba gaba daya.

Ya ci gaba da bayanin cewa, kwamashinan ’yan sanda jihar CP Morris Dankombo ya aike da ’yan sandan musamman na kwantar da tarzoma zuwa yankin domin tabbatar da wanzar da doka da oda, yayin da tuni kuma sashen binciken laifukan ta’addanci a rundunar ya fara gudanar da bincike da zummar kamo wadanda suke da hannu.

Ya ce, kuma rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi. (Garba Abdullahi Bagwai)